Karamar hukumar mulkin Mandera a kasar Kenya ta rufe kan iyakokinta daga daren jiya Laraba har tsawon makonni uku bisa umurnin Ministan kula da al’amuran cikin gidan kasar, Fred Mating'i saboda ana kara samun masu kamuwa da cutar coronavirus a kasar.
Matakin killacewa na baya-baya da kasar ta dauka ya haramta zirga-zirgar motoci da jiragen sama a ciki da wajen yankin.
Bugu da kari, Matiang’i ya ce cibiyar tsaro game da annobar coronavirus ta Kenya na duba yiwuwar sanya matakan kare lafiyar al’umma a kananan hukumomin mulkin Mumbasa, Kwale da Kilifi.
Hukumomi a Kenya sun dage wajen sa ido don tabbatar da cewa mutane suna kiyaye matakan kariya da aka sanya a yayin da Shugaba Uhuru Kenyatta ya bayyana cewa jami’an tsaro na kokarin gano wasu mutane da yawa da suka tsere daga cibiyoyin killacewar da aka ajiye su a birnin Nairobi.
A halin yanzu, hukumomin Kenya sun ce an samu karin mutane 7 da suka kamu da cutar coronavirus a ranar Laraba 22 ga watan Afrilu, abinda yasa jimillar wadanda suka kamu da cutar a kasar ya kai 303. Ya zuwa yanzu an samu rahoton mutuwar mutane 14.
Facebook Forum