Hukumomi a kasar Botswana sun ce baki dayan ‘yan majalisun kasar da suka hada har da shugaban majalisar dattawa da ta wakilai suna a cikin zaman kulle na tsawon kwanaki 14 daga yau Juma’a, kwana daya bayan wani gwaji da aka sami wani jami’in kiwon lafiya na majalisar ya kamu da cutar Coronavirus.
Wata sanarwar gwanatin ta ce jami’in na cikin mutane na 7 sababbin kamuwa da cutar a kasar da ke yankin kudancin Afrika, wanda ya kara adadin masu cutar a kasar zuwa 13.
Shugaban kasar Eric Masisi, ya koma bakin aikin tun a farkon watan nan na Afrilu, bayan killace kansa da yayi, sakamakon wani balaguro da yayi a makwabciyar kasar Namibiya a watan da ya gabata. To sai dai an gwada shi ba ya dauke da cutar ta COVID-19 a ran daya ga watan Afrilu.
Tuni da Masisi ya kafa dokar gaggawa tare da dukar matakan hana yaduwar cutar, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutum daya.
Facebook Forum