Daraktan hulda da manema labarai na sashen aikace aikacen shelkwatar tsaron Najeriya, Manjo Janar John Enanche, ya ce duba da yadda cutar coronavirus ke yaduwa, rundunar tsaron kasar ta yi wani shiri na ko-ta-kwana don kare farar hula da sojojin kasar daga wannan cuta.
Da yake yi wa Muryar Amurka karin bayani, kwamanda a rundunar sojin ruwan Najeriya Abdulsalam Sani, ya ce akwai wasu asibitoci guda goma sha bakwai na sojoji da aka kebe a shiyoyin kasar shida don tunkarar wannan cuta. Ya kuma ce tuni aka riga aka fara amfani da wasu daga cikin asibitocin wajen gudanar da bincike kan wannan cuta ta COVID-19.
Rahotanni sun bayyana cewa wani jami'in rundunar da ya dawo daga kasar waje kwanan nan ya kamu da cutar coronavirus kuma yana samun kulawa a asibiti. Yayin da wasu karin jami’an soji da suma suka dawo daga kasar waje suka killace kansu.
Manjo Janar Eneche ya ce sojojin Najeriya zasu ci gaba da tallafa wa fararen hula wajen tunkarar wannan cuta da ta zama alakakai.
Ga karin bayani cikin sauti.