Sallar Eid-el-Fitr wacce aka gudanar bayan azumin watan Ramadana na bana ta zo a wani yanayi na rashin walwala saboda matakan da gwamnati ta sanya don yaki da cutar COVID-19.
A Fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na daga cikin wadanda suka gudanar da sallar Idi a gida, tare da iyalansa.
A cikin hotunan da fadarsa ta fitar, an nuna shugaban yana sallah da wasu mukarrabansa da kuma iyalansa, dukkaninsu sanye da takunkuman fuska.
A jihar Filato, an gudanar da sallar ne cikin ni’ima ta ruwan sama, yayin da wasu suka gudanar da sallar a masallatai, wasu kuwa sun yi sallar ne a gidajensu da iyalansu kamar yadda hukumomi suka ba da umurni.
Wasu da wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji ta zanta da su sun bayyana mata cewa, duk da rashin walwala, sun ce an gudanar da sallar cikin koshin lafiya.
A jihar Kano kuwa, sabanin wasu jihohi a Najeriyar, an gudanar da sallar Idi yadda aka saba.
An gudanar da sallar ne a filin Kofar Mata da ke Kano, kuma sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ne ya jagoranci sallar.
Manyan mutane da dama kamar gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, da wasu mukarraban gwamnatinsa sun hallarci sallar, sanye da takunkuman fuska, da kuma tazara tsakanin sahunsu.
A jihar Kaduna, inda gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufai ya kakkaba dokar zama a gida ranar sallah, ba a gudanar da sallar Idi ba.
Lamarin dai ya janyo wa gwamnan suka daga mutane da dama.
Kamar sauran jihohi, an sanya wannan dokar ne domin takaita yaduwar cutar coronavirus a kasar.
Mutane da dama sun ji ba dadi saboda rashin shagulgulan sallah kamar yadda suka saba, inda suke cewa ko kakaninsu ba su taba fuskantar irin wannan yanayi ba.
Duk wannan na faruwa ne sakamakon cutar Coronavirus wacce ta kama mutum 7839 a kasar yanzu kamar yadda hukumar kare yaduwar cututtaka ta NCDC ta fitar.
Facebook Forum