Masu gabatar da kara sun ce barnar da kungiyar 'yan tawaye da yake yiwa jagoranci wacce ake kira UCP a takaice tayi , a gabashin jamhuriyar demokuradiyar kwango tsakanin shekara ta 2002-2003, duk yana kansa.
Ntaganda yana fuskantar tuhuma daban daban har 13 na laifuufkan yaki da suka hada da cin zarafin Bil'Adama, da kisa, da fyade, da tilastawa yara aikin soja, da kuma tilastawa jama'a barin muhallansu.
Ana zargin cewa hare haren da kungiyarsa ta kai a lardin Ituri an auna su musamman kan kabilun Lendu, da Bira, da Nande. Daya daga cikin wadanda ake zargin hada baki wajen kitsa hare haren tareda Ntatanga, shine Thomas Lubanga, wanda aka daure shi shekaru 14 a gidan yari a shekara ta 2012, bayan da aka sameshi da laifin tilastawa yara aikin soja.
Hakan nan babbar kotun tana binciken zargin da ake yiwa Ntaganda da mayakana sakai da yake yiwa jagoranci suka aikata a lardin Kivu ta kudu, amma wannan baya cikin shari'ar da ake yi masa ahalin yanzu.