Kakakin rundunar sojojin yankin Manjo Dieudonne Kasereka ya bayyana cewa, da misalin karfe biyu na safe, wasu 'yan bindiga dauke da makamai suka kai wa sansanin 'yan China din hari a kauyen Mukera da ke yankin Fizi na lardin Kivu ta Kudu.
“Mutum 14 ne maharan suka tafi da su, biyar daga ciki, an kai su zuwa wani wuri da ba a san inda suke ba,” in ji shi, ya kara da cewa sauran taran kuma an kwashe su kuma suna cikin koshin lafiya.
Kanal David Epanga, shugaban rundunar soji a Fizi, ya ce dan sanda daya ya rasa ransa a harin.
Ma'aikatan 'yan kasar China biyar da aka sace, ma'aikatan wani kamfani ne da ke aikin hakar gwal a yankin na tsawon watanni hudu zuwa biyar, in ji shugaban kungiyoyin fararen hulan Fizi, Lusambya Wanumbe.
A cikin watan Agusta, hukumomin Kivu ta Kudu sun dakatar da ayyukan kamfanonin da ke samun kudi daga China, bayan da mazauna yankin suka zarge su da hako zinari ba tare da izini ba da kuma lalata muhalli.