Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Niger, Dr Ibrahim Sule, ya bayyana cewa an gano cutar a karamar hukumar Edati na jihar.
Bisa ga cewar kwamishinan, cutar ta bazu zuwa a kananan hukumomin jihar guda goma sha biyu. Ya kuma ce gwamnati ta tura magungunan rigakafi zuwa ga karamomin hukumomin domin yaki da cutar.
Dr. Sule ya bayyana cewa cutar tana yaduwa ne, saboda haka ya yi kira ga jama’a su yi maza su yi rigakafi.
Jihar Naija na daya daga cikin jihohin da suka sami lambar yabo a saboda ci gaban da ta samu a yaki da ciwon Polio, a wata gasa da gwamnoni suka shirya tare da goyon bayan gidauniyar Bill Gate da nufin yaki da cutar Polio.