A jiya ne Kamfanin Facebook ya shaida cewar yana tsammanin ya fitar da adireshin sakon email na wasu miliyoyin mutane bisa kuskure.
An dai kiyasta sama da mutane milliyan 1.5 kamfanin ya wallafa adireshin email din nasu daga watan Mayun shekarar 2016 zuwa yanzu, wanda hakan shine sabon danbarwar rikicin ajiyar bayanan sirri da kamfanin ya sake shiga a nan kusa.
Tun a watan Maris kamfanin na Facebook ya daina amfani da adireshin email, wajen tantance masu bukatar bude sabon shafi, kamfanin yace tuni ya dakatar da hakan, domin kuwa ana amfani da adireshin na mutane wajen yin wasu abubuwa da basu kamataba.
Kamfanin Facebook ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters, cewa an magance matsalar, da kuma inganta dukkan manhajojin su da bata gari ke iya shiga don satar bayanan sirri.
Facebook Forum