A wani taron manema labarai da ta kira yau a birnin tarayya Abuja, cibiyar raya demokradiyya da cigaba, wato Center for Democracy and Development, ta koka bisa yadda mutane da yawa suka zama malaman zabe ta kafar yanar gizo.
Da ya ke yiwa Muryar Amurka karin bayani jim kadan bayan taron, wakili a cibiyar Dr. Abubakar Kari, ya ce illar yada sakamakon zabe na bogi shine ko da na gaskiyar ya fito ba lallai mutane su amince da shi ba.
Dr. Kari ya ce ko da yake hukumar zabe kadai ke da alhakin bayyana sakamakon zabe, jan kafar da ta keyi ya sa wasu mutane ke yin riga malam masallaci.
A cewar Dr. Sani Adam Abdullah, wasu lokutan kafafen yanar gizo na kawo illa bisa yadda wasu ke amfani da su wajen watsa bayanan bogi.
Irin wannan matsalar ce ta sa kasashe irin su Zimbabwe da Congo a kwanakin baya suka toshe kafafen yanar gizo lokacin da suka gudanar da zaben su.
Facebook Forum