Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cibiyar Amurka Na Shirin Kashewa Matan Afirka Miliyoyin Daloli


Mai ba da shawara a Fadar gwamnatin Amurka, Ivanka Trump yayin ziyarta a Habasha
Mai ba da shawara a Fadar gwamnatin Amurka, Ivanka Trump yayin ziyarta a Habasha

Wata cibiyar Amurka ta ce ta na shirin kashe daruruwan miliyoyin daloli, a wasu nau’ukan kasuwancin da ka iya tayar da komadar mata a Afirka.

Diyar Shugaba Donald Trump, wato Ivanka Trump, da kuma mukaddashin shugaban hukumar saka jari a kasashen waje (OPIC a takaice), David Bohigian, su ne su ka bayar da wannan sanarwar jiya Litini a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, inda su ma wani bangare ne na wata tawagar gwamnatin Amurka da ta je ziyara.

Wata takardar bayani daga OPIC ta ce burin shirin na “2X Africa” shi ne ya tara dala bilyan daya ya kuma saka jarin dala miliyan 350 kai tsaye, a kamfanoni da kuma gidauniyoyi mallakin mata kuma wadanda mata ne ke shugabantarsu, ko kuma ta samar da kayayyaki da harkoki, wadanda tabbas za su amfani mata a nahiyar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG