Majalisar Dinkin Duniya ta ce, rundunar hadin gwiwa ta MINUSCA na gudanar da bincike, domin zakulo wanda ya aikata kisan a Bangui, wanda har ila yau ya raunata wasu dakaru takwas.
Mr Ban, ya kuma yi kira da kakkausar murya da a yi maza maza a cafke wanda ke da alhakin kisan, domin a gurfanar da shi a gaban kuliya, ya kuma yi kira ga mutanen kasar da su rinka mutunta rundaunar ta MINUSCA ganin cewa bata nuna banbanci a ayyukanta.
Dakarun Majalisar Dinkin Duniya sun karbi ragamar wanzar da zaman lafiya ne daga hanun rundunar tsaron hadin gwiwa ta Tarayyar Afrika a bara, da zimmar samar da tsaro ga fararen hula da kuma tabbatar da mika mulki ga zababbiyar gwamnati.
A dai watan Oktoba mai zuwa a ke sa ran za a gunadar da zaben.
A shekarar 2013 kasar ta Jamhuriyar Tsakiyar Afrika ta tsudnuma cikin rikicin siyasa, bayan da ‘yan tawaye wadanda mafi yawansu Musulmai ne suka kifar da gwamnatin Francois Bozize, tare da cin zarafin bil adama, lamarin da ya samar da mayakan sa kai a bangaren kiristoci, wadanda suma suka rinka daukar fansa.