Abinda ke nuna hakan shine ziyarar da shugaban rundunar sojin kasa na Najeriya laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ke kai wa rundunonin sojin domin jin halin da yanayin tsaro ke ciki.
Wannan na zaman wani bangare na kai ziyara rundunonin da ke yaki da ‘yan ta'adda a karkashin shirin Sahel Sanity a arewa maso yammacin Najeriya.
A lokacin ziyarar da ya kai a yankin na 8 da ke rundunar sojin ta Sokoto, babban hafsan na mayakan kasa ya duba wasu ayyukan da ake aiwatarwa a barikin sojin Giginya wadanda ke da manufar kyautata jin dadin jami'an soji.
Hakan kuma yana zuwa ne a daidai lokacin da jami'an sojin ke cikin daji suna fafatawa domin kawar da ayyukkan ta'addanci a yankin gabashin Sokoto.
Masanin Harkar Tsaro Detective Auwal Bala Durumi Iya, ya ce irin wannan ziyarar ta na da tasiri wajan zaburar da mayakan da ke fagen fama, inda zai ji ta bakin su domin ya kara musu karfin gwiwa kana ya ji matsalolinsu kuma ya bayyana musu abin da ya ke so.
Suma mazauna yankin gabashin jihar Sokoto inda lamari tsaro ya tabarbare a kwanakin baya sun yaba da yadda yanayi tsaro ya fara inganta a yankin nasu inda 'yan kasuwa da manona suke gudanar ayyukan su.
Sai dai kuma bayanai na nuni da cewa ana samun ayyukan ta'addanci jefi-jefi a wasu kananan hukumomin jihar ta Sokoto.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:
Facebook Forum