Ministan kula da ayyukan 'yan sanda Muhammadu Maigari Dingyadi wanda ya tabbatar da hakan yace karin wa'adin, zai baiwa gwamnati damar kimtsawa domin zakulo wanda zai maye gurbin Adamun.
A cikin hirarsa da manema labarai, ministan 'yan sanda Muhammadu Maigari Dingyadi ya ce gwanmati za ta sanar da wanda zai maye gurbin babban sufetan 'yan sandan nan ba da jimawa ba.
Shi dai sufeto janar din wanda zai cika shekaru sittin ranar sha bakwai ga watan satumba, an nada shi ne ranar sha Biyar ga watan janairun shekara ta dubu biyu da sha tara bayan wanda ya gada Ibrahim Idriss yayi ritaya.
sufeto-janar-na-yan-sandan-najeriya-ya-gurfana-gaban-majalisar-dattawa
za-a-maye-gurbin-rundunar-sars-aig
buhari-ya-ba-sufeton-yan-sanda-umarnin-kawo-karshen-cin-zarafin-jama
Ranar litinin ta wannan mako ne wa'adin sufeto janar din ke karewa, amma fadar gwamnatin bata ce kome akai ba al'amarin da ya haddasa yada jita jita akan batun har da wadansu suka rika wallafa labaran kanzon kurege tare da nuna hoton wani da suka ce wai shi aka nada a matsayin sabon sufeto, kafin daga baya aka karyata labarin.
A halin da ake ciki kuma, wani babban lauya a Najeriya Ebun Adegboruwa, ya kalubalanci kara wa’adin aikin sufeta janar din ‘yan sandan. Bisa ga cewarsa, yin haka ya sabawa kundin tsarin mulki kasa. Yace ba za a iya karawa Sifeta janar Mohammed Adamu wa’adin mulki ba domin ya cika shekaru 35, wa’adin da doka ta bashi na aikin ‘yan sanda.
Babban lauyan ya ambaci sassan doka na 215 da 216 da suka yi bayani dalla dalla kan sharudan kafa Majalisar ‘yan sanda da kuma abinda ya shafi aikin ‘yan sanda.
Ebun Adegboruwa yace bisa ga tsarin dokar kasa da kundin tsarin mulkin kasa ya tanada “ Shugaban kasa bashi da ikon sake dawo da jami’in dan sandan da ya yi ritaya ya sake maida shi aikin ‘yan sanda ta wajen kara mashi wa’adin aiki”
Babban lauyan ya kara da cewa, “Shugaban kasa ba zai iya zaben babban sufeta janar na ‘yan sanda ko kuma karawa sufeta janar na ‘yan sanda da ya yi ritaya wa’adin mulki ba, ba tare da shawarar Majalisar aikin’yan sanda ba, wadda a wannan halin ba ta yi wani zama a kan wannan batun ba balle ta amince da kara mashi wa’adin aiki.” Sabili da wadannan dalilan, babban lauyan ya ce a halin yanzu, Najeriya bata da babban sufeta janar na ‘yan sanda da doka ta halalta.”