Bayan tashin hankalin da ya yi sanadin asarar dinbin rayuka da dukiyoyi a makon jiya a jahar Kaduna, yau Talata Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kai ziyayar jajantawa jahar da al’ummarta. A jawabinsa, Shugaba Buhari ya ce, “Bari in fara da bayyana matukar bacin raina kan rasa rayuka da dukiyoyi sandaiyyar tashin hankali na baya-bayan nan.”
Buhari ya ce da tashin hankalin farko da kuma wadanda su ka biyo bayan na farkon duk babu dalilin yinsu. Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga al’ummar jahar Kaduna da Masarautar Adara saboda rasuwar Agwam Adara, Dr. Maiwada Bature, wanda wasu masu sace mutane don neman kudin fansa su ka kashe shi bayan an tura ma su kudin fansar. Buhari ya yaba da gaggauta daukar mataki da gwamnan jahar Kaduna Nasiru El-Rufa’I ya yi, ya na mai tabbatar da cewa gwamnatin tayayyar najeriya ta tanaji isassun jami’an tsaro don magance matsalar ta Kaduna.
To sai dai wani dan masarautar Adara mai suna John Danfulani, ya ce ziyarar da Buhari ya kai Kaduna ta yi kyau amma da ya zarce masarautar Adara ya yi jajen rasuwar Sarkinsu da ziyarar ta fi kayatarwa. Ya ce an yi ta samun matsaloli da dama a kudancin Kaduna. Mr. Danfulani ya yi kira ga ‘yan jahar da su kai zuciya newa, su tabbatar da zaman lafiya tsakanin juna.
Ga wakilinmu a Kaduna, Nasiru Birnin Yero, da cikakken rahoton:
Facebook Forum