Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki a jahar Kebbi, inda zai jaddada muhimmancin noman rani da sauran nau’ukan noma da sana’a. hasali ma ya kaddamar da noman ranin a jahar ta Kebbi, wacce ita aka zaba wannan shekarar don kaddamar da noman ranin. Baya ga haka ma Shugaba Buhari ya kaddamar da wani shiri na bayar da tallafi ga manoma.
Wannan shiri na bayar da tallafi ga manoma ya dan banbanta da wanda aka zaba gani saboda sabanin shirin baya na bai wa manya da matsakaitan manoma, wannan shiri na musamman na baiwa kananan manoma tallafi ne.
Babban Bankin Najeriya da hadin gwiwar gwamnatin tarayyar najeriya ne ke daukar nauyin wannan shirin. Wakilinmu y ace wannan ne karo na farko da aka kaddamar da shiri irin wannan, wanda gwamnati mai ci ke kokarin ganin nasararsa wajen karfafa kananan manoma. Wakilinmu y ace an zabi jahar Kebbi don kaddamar da shirin ne saboda it ace jahar da ta fi noman shinkafa da alkama, wadanda aka fai ci a Najeriya.
Ga wakilinmu na Shiyyar Sakkwato Murtala Faruk Sanyinna da cikakken rahoton: