Hare haren sun tilastawa kamfanin samarda wutar lantarki na YEDC dake kula da jihohin Adamawa, Borno da Yobe da kuma Taraba rufe ofisoshinsa ban da asarar dimbin kayan da kamfanin yayi.
Lamarin ya sa jihohin sun samu matsalar samun wutar lantarki. Alhaji Ahmed Hassan Ardo jami'in hulda da jama'a na kamfanin yace yanzu haka kamfanin na cikin wani mawuyacin hali na rashin kudaden shiga. Duk ofisoshinsu dake Borno sun rufe saidai Biu da Maiduguri. Da sukan samu nera miliyan dari da ashirin daga jama'a amma yanzu da kyar suke samun miliyan biyar zuwa shida.
A Yobe duk da wai basu rufe ofisoshinsu ba amma akwai wasu wurare da ba zasu iya zuwa ba kamar su Gujuba da Buni Yadi da sauran wuraren a Yobe dake hannun 'yan Boko Haram. Bamabaman da aka jefa a Damaturu da Potiskum sun shafi ayyukan kamfanin. Da kyar kamfanin ke samun kudin yin aiki.
Hare-haren Boko Haram sun kuma durkusar da harkokin kasuwanci a jihohin. Rufe wasu iyakokin kasar da Kamaru shi ma ya dakatar da hadahadar kasuwanci da aka saba yi a wuraren.
Ga karin bayani.