Majiyoyi daga yankunan da lamarin ya shafa sun ce maharan sun umarce su da kar su yi biyayya ga duk wata hukuma ko gwamnati a jihar ta Neja.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani ganau a yankin da ya bukaci a sakaya sunansa ya na bayana cewa, sun sami labari daga yan uwansu da ke zaune a cikin kauyen Kawure inda tsohon dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Neja ta gabas, David Umaru ya fito.
Ya kuma kara da cewa rundunar hadin gwiwa ta sojojji ta yi kokarin tarwatsa mayakan daga kauyen Kawure a baya, amma bayan wani kankanin lokaci sai suka sake taruwa a garin, kasancewar sansanin sojoji ba nan ya ke ba.
Majiyoyi daga yankin dai sun yi nuni da cewa a halin yanzu ba a kauyen Kawure kadai ne mayakan suka mamaye ba har ma da kauyuka kamar Kuregbe, Awulo, da sauransu.
A cikin kauyukan Awulo da Kuregbe, mayakan sun tara mazauna yankin da suka hada da musulmai da kiristoci, sannan suka ba su umarnin cewa duk yarinyar da ta kai shekara 12 a yi mata aure.
"A halin yanzu babu wata doka ta gwamnati da ke aiki a yankin ban da na mayakan Boko Haram" a cewar wasu majiyoyi daga yankin.
Wani mazaunin garin ya ce mayakan suna cin karensu ba babaka a yankin kuma sun ce kar wanda ya kai karar duk abin da ya faru ga 'yan sanda ko kotu ko wata hukuma da aka kafa don yanke hukunci.
Suleiman Chukuba da ke zaman shugaban karamar hukumar Shiroro ya tabbatar da kwararar 'yan Boko Haram zuwa yankin, yana mai cewa lamarin ya shafi wurare hudu ne.
"Dalilin da ya sa al’ummar yankin suka yi imanin cewa mayakan Boko haram ne suka mamaye su, ba ya rasa nasaba da salon da mayakan suka bullo da shi na fadawa mutanen gari cewa suna da kudin da za su taimaka musu kuma suna da bindigogin da za su ba su don yakar gwamnati. Sai dai ba su fara tilsatawa al’ummar yankin su bi akidarsu ba" in ji Chukuba.
Idan ana iya tunawa rahotanni daga yankin Arewa maso gabas a lokacin da hare-haren mayakan boko Haram suka yi kamari, irin wannan koyarwa ce aka sani da mayakan don samun mabiya.