Kusan ana iya cewa wayar hannu da kwamfuta babu kasar da za aje babu su, sun zama ruwan dare a duniya. Mutane kuwa sun auri wadannan na’urorin kamar yadda suke gudanar da ibadun su.
Wani bincike ya gano cewar yawaita amfani da wadannan na’urorin na haddasar da wasu cututtuka da mutane basu lura da abun da ke kawosu. Dr. Lushnath Gunasekera a jihar Orlando ta Amurka, ya wayi gari baya jin dadi.
Koda ya kai kansa asibiti, an duba shi kuma an tabbatar da cewar cutar da ke damun shi tana da nasaba da yadda yake kallon kwamfuta, da wayar hannu, ta yadda baya samun motsa jikin shi.
A duk lokacin da mutum ya maida kallon kwamfuta batare da daukar lokaci don hutu ba, to babu shakka zai iya samun cutar da zata hada da mutuwar bangare daya na jiki.
Sabo da yadda mutane ke amfani da jiki da ido wajen maida hankali suna kallon na tsawon lokaci, hakan yana sa wasu jijiyoyin jiki su sankare a wani yanayi, muddun kuma jikin ya saba da haka to babu shakka jikin na iya kamuwa da cututuka masu nasaba da mutuwar rabin jiki.
Masana irin su Nathaniel Melendez, wanda ya kware a wajen motsa jiki, ya tabbatar da cewar duk lokacin da mutum zai dinga juya yadda yake kallon kwamfuta da ma waya daga lokaci zuwa lokaci, kana da motsa jiki na kimanin minti 30 a kullun, to hakan zai taimaka wajen hatsarin kamuwa da wasu nau’ukan cututtuka da wadannan na’urorin ke zama sanadiyar haddasuwar su.
Facebook Forum