Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bidiyon Da Boko Haram Ta Fitar Na Bogi Ne - Rundunar Sojin Saman Najeriya


Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji.
Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji.

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta musanta ikirarin da kungiyar Boko Haram ta yi, na daukar alhakin kakkabo jirgin saman sojinta na NAF Alpha-Jet.

Wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a da watsa labarai na rundunar ta sojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar, ta bayyana hoton bidiyon da ke zagayawa a kafafen sada zumunta mai nuna ‘yan bindigar sun harbo jirgin, da cewa na jabu ne.

Air Commodore Edward Gabkwet, Kakakin Rundunar Sojin Saman Najeriya
Air Commodore Edward Gabkwet, Kakakin Rundunar Sojin Saman Najeriya

A ranar 31 ga watan Maris ne jirgin saman na NAF Alpha-Jet mai lamba NAF-475 YA bata, tare da mutane biyu a cikinsa.

Boko Haram ta saki wani hoton bidiyo da ke nuna wasu mayaka suna harbin jirgin sama, kana kuma aka ga tarwatsewar wani jirgin daga sama ya kuma fado a kasa.

Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji
Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji

To sai dai Gabkwet ya zargi ‘yan ta da kayar bayan da harhada hotunan, tare da nuna wani waje da jirgi ya tarwatse a sararin samaniya, saboda “yada farfagandar karya.”

Ya ce “duk da yake ana ci gaba da binciken kwakwaf akan bidiyon, amma a bayyane yake cewa an harhada hotunan bidiyon ne domin ba da sakon cewa an harbo jirgin ne.”

Karin bayani akan: Boko Haram, Jirgin Yakin Saman, jihar Borno​, Sojojin Najeriya, Nigeria, da Najeriya.

Air Commodore Edward Gabkwett ya ci gaba da cewa “hoton bidiyon ya kasa bayyana dangantaka ko alaka tsakanin jirgin saman da ya tarwatse a sama, da kuma masu harbi a kasa, wadanda alamu suka nuna cewa suna auna wani abu ne a kasa ba a sama ba.”

Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji
Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji

“Haka kuma ba zai yiwu jirgin ya tarwatse tun daga sararin samaniya kamar yadda bidiyon ya nuna, ya fado kuma har a sami sauran karikice masu girma da aka gani a hoton ba, inda bangaren baya na jirgin ya ke a hade” Gabkwet ya ci gaba da bayyanawa, “hakika irin wannan tarwatsewar za ta sa jirgin ya yi kwara-kwara, kuma ya watsu a wurare daban-daban na tsawon kilomitoci.”

Akan haka ya ce wannan farfaganda ce kawai da ‘yan kungiyar suka kitsa, wadda kuma ke zuwa a daidai lokacin da dakarun Najeriya suke kara dakushewa da karya lagon kungiyar mayakan.

Rundunar sojin na sama sun yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su amince da hoton bidiyon da ke zagayawa har sai an kammala cikakken bincike akan faduwar jirgin saman tukunna.

XS
SM
MD
LG