WASHINGTON D.C. —
Dan wasa Christian Benteke na club din Crystal Palace a Ingila, ya ce, yana so ya ci gaba da zama a club dinsa, duk da sha'awar da club din dan wasa Marouane Fellaini na kulob din Shandong Luneng Taishan da ke China ta nuna akansa.
Club din mai buga wasa a babbar gasar Super League ta China, ta nuna sha'awar sayen dan wasan dan asalin kasar Belgium kan kudi fam miliyan £15- kwatankwacin dalar Amurka miliyan $19.
Amma Duk da haka, dan wasan mai shekaru 28, ya gwammace ya ci gaba da zama a London, domin ya nuna kwarewarsa ga manajan Crystal Palace Roy Hodgson, bayan shekaru biyu da ya kwashe yana fadi-tashi a filin wasan kungiyar na Selhurst Park.
Facebook Forum