WASHINGTON, D.C. —
Barcelona na shirin tayin karshe ga dan wasa Chelsea Willian, wanda da jimawa kungiyar ta Barcelona ta sa ido akan dan wasan dan asalin kasar Brazil din.
Rahotanni sun nuna cewa, klub din na Catalan ya shirya tsaf kan tayin na kusan fan miliyan 20.
Kwantaragin Willian ba zai kare ba har sai a karshen wannan kakar.
Tattaunawa game da sabon kwantiraginsa bai kai matakin karshe ba a yanzu, kuma tana iya yiwuwa Blues za ta iya aminta da hakan a cikin wannan watan.
Barcelona ta taba gabatar da tayin fam miliyan 55 ga Willian a lokacin bazara a shekara ta 2018.
Facebook Forum