Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta kammala yarjejiniyar sayen matashin dan wasan tawagar kasar Ingila, na 'yan kasa da shekara 16 (Under 16) mai suna Louie Barry, bisa kwantiragin shekara 3 daga kulob din West Bromwich Albion.
Dan wasan Barry ya fara wasansa tun yana dan shekaru 6 a kungiyar ta West Brom, bangaren matasa sai dai ya ki amincewa ya bugawa babbar kungiyar tasa.
Wannan cinikin zai sa West Brom su samu kudin da ya kai fam dubu £235,000 daga Barcelona, a matsayin ladar dan wasan kamar yadda kamfani dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Dan wasa Barry zai buga wasane a kungiyar matasa na 'yan kasa da shekaru 19, a Barcelona a kakar wasa mai zuwa kafin daga bisani ya shiga cikin tawagar manya kulob din.
West Brom tare da hukumar kula da kwallon kafa ta Ingila wato (FA) sai sun amince da cinikin, wanda hakan shine zai tabbata sayen a hukumance.
Barca ta ce sayen matashin dan wasan Barry alherine a gareta, domin daya daga cikin kwararrun matasan 'yan wasan kwallo kafa a kasar Ingila lura da yadda yake fafata wasa a yanzu haka.
Facebook Forum