Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bankin AFDB Zai Tallafawa Shirin Samar Da Iskar Gas A Mozambique


Ginin bankin AFDB a birnin Abidjan
Ginin bankin AFDB a birnin Abidjan

Bankin tallafawa ci gaban kasashen Afirka AFDB ya bayyana cewa zai shiga sahun wasu bankunan duniya domin samar da dala bililiyan 20 ga shirin iskar gas na kamfanin LNG a Mozambique.

Bankin ya ce ya kammala shirin bayar da na shi kason talaffi da bashin dala miliyan 400.

Shugaban bankin AFDB
Shugaban bankin AFDB

Shirin na iskar gas na LNG a Mozambique wanda ake sa ran zai ci dala biliyan ashirin shi ne jarin kasar waje ma fi girma kawo yanzu a nahiyar Afirka.

Aikin zai kunshi har da jiragen kasa masu tsawo guda biyu da za su rinka safarar tan miliyan 13 na iskar gas a kowace shekara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG