Bankin Raya Afirka da ake kira AFDB a takaice, na shirin kashe zunzurutun kudi har dalar Amurka miliyan 500 don bunkasa masana'antu na musamman don taimaka wa ci gaban harkar noma a Najeriya.
Baban Darakta a bankin na AFDB, Mr. Ebrima Faal, ya ce sun bullo da tsarin na bunkasa aikin noma a Najeriya ne saboda sassan Afrika da dama suna fitar da muhimman albarkatun kasa zuwa ketare domin a sarrafa su kana a sake dawo da su, yin hakan na kawo kashe kudaden musaya masu yawa a cewarsa.
Daraktan ya kuma ce suna duba Najeriya a matsayinta babbar kasa a Afrika kuma mai karfin tattalin arziki da albarkantu kasa, don ganin yadda zasu canza salon tsarin noma wanda ake yi don a ci, zuwa wanda ake yi da yawa har a saida wa masana’antu a kuma kirkiro ayyukan yi.
A bangaren gwamnatin Najeriya, Ministan ma'aikatar Noma Alhaji Muhammad Sabo Nanono, ya ce duk kananan hukumomin Najeriya zasu samu wannan damar, domin bunkasa harkar noma.
Aliyu Abbati Abdulhameed, babban daraktan hukumar NIRSAL, wadda babban bankin Najeriya ya kirkira don bunkasa harkar noma da tallafa wa manona a Najeriya, ya ce wannan tsarin zai taimaka wa kananan manoma ta yadda za a yi noma a kuma sarrafa kayan gonan duk a wuri daya ba sai an kai kasashen waje ba.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum