Kowacce shekara a taron kolin kungiyar hadin kan kasashen nahiyar Afrika AU, kungiyar takan zabi daya daga cikin membobinta ya zama shugaban jeka na yika, wanda galibi ake kira shugaban kungiyar tarayyar Afrika. A bana, mai yiwuwa ne shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ne zai hau kujerar.
Yves Niyira-gira yana aiki da Fehamu, wata hadakar kungiyar kasashen Afrika mai fafatukar neman ganin an yi adalci. Yace zabar Mugabe ya shugabanci kungiyar AU zai haifar da mummunan sakamako ga ‘yan Afrika.
Yace muna kira ga taron shugabannin kasashen da gwamnatoci, su zabi wanda yake da akidar shugabancin kwarai, mai kare hakkokin bil’adama, da kiyaye doka da oda, da kare damokaradiya kamar yadda yake a manufofin kungiyar hadin kan kasashen Afrika.
Shugaba Mugabe ya yi mulki a Zimbabwe na kusan shekaru talatin da biyar. Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun ce yana cigaba da rike madafun iko ne ta hanyar magudin zabe, da tozartawa abokan hamayya.
Ana tababa musamman a kan sake zabensa. A zaben da aka gudanar a shekara ta dubu biyu da takwas ya haifar da tashe tashen hankali da takaddama.
Sai dai yana da abokai a kungiyar hadin kan Afrika. Sau da dama ana ambaton kungiyar nahiyar da suna “kungiyar ‘yan mulkin kama karya”. Hadakar kungiyar Fehamu tace, shugabannin kasashen nafiyar Afrika goma sha hudu da suka fi dadewa bisa karagar mulki sun hadu sun yi mulki na tsawon shekaru dari uku da ishirin da uku tsakaninsu.
Shugabannin kasashe biyu, shugaban kasar Angola Jose Eduardo dos Santos da na kasar Guinea Teodoro Obiang Ngume sunfi Mr. Robert Mugabe dadewa bisa karagar mulki.
Yayinda za’a gudanar da zabe a kasashe goma na nahiyar Afrika bana, Niyi-ra-gira na kira ga kungiyar hadin kan kasashen Afrika tayi tsayin daka wajen ganin an gudanar da zabuka masu sahihanci.
Yace mun lura da wani salo inda shugabannin kasashe da gwamnatoci suke kokarin sauya kundin tsarin mulki, ko kuma su nemi kara wa’adin mulkinsu a kasashe da dama.
An yi wannan yunkurin a Burkina Faso amma bai yi nasara ba. An yi haka kuma a kasashe da dama, kamar Burundi da Damokaradiyar Jamhuriyar Kwango, da kasar Kwango, da Benin da Saliyo da kuma wadansu kasashe da dama dake kokarin daukar wannan matakin.
Kungiyar hadin kan kasashen nahiyar Afrika tayi watsi da zargin da ake yi mata cewa bata goyon bayan gudanar da sahihin zabe. Kungiyar na cewa tana tura masu sa ido a kasashen da ake gudanar da zabuka, da kuma shawartar kasashe kan matakan da zasu dauka na shawo kan matsalolin zabe.
Sai dai biyo bayan wadansu abubuwa da suka taso na ba zata, shugaban kungiyar hadin kan kasashen nahiyar Afrikan ka iya kasancewa wanda yake mulkin kama karya a kasarsa, wanda yake cigaba da shan suka daga kungiyoyin kare hakin bil’adama.`