Wani baturen ‘yan sanda dake wurin da abin ya faru yace an boye bam din ne a karkashin motar Muhidin Mohammed Haji Ibrahim, tsohon ministan tsaro wanda a yanzu yake aiki a zaman mai bayar da shawara ga majalisar dokokin Somaliya. Bam din ya tashi yau litinin a wata unguwa da ake kira KM4.
Ibrahim dai dan wata jam’iyyar siyasa ce mai suna Kulan.
Shugaban jam’iyyar ta Kulan, Abdulkadir Barnaamij ya fadawa sashen harshen Somaliya na Muryar Amurka cewa wannan harin bam da aka kai ma Ibrahim ya faru ‘yan sa’o’i kadan a bayan da ya halarci wani taron jam’iyyar a Mogadishu.
Babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai wannan hari har ya zuwa yanzu, amma harin yana kama da irin wadanda kungiyar al-Shabab take kaiwa.
Tsageran kungiyar masu alaka da al-Qa’ida su kan kai hare-hare a kan jami’an gwamnati da sojojin kiyaye zaman lafiya na Tarayyar Afirka.