A cikin karar da ya shigar ta hannun babban lauya Festus Kyamo Bala Ngilari yace takardar da aka ce ya mika ta murabus shi bai mikawa majalisar dokokin jihar Adamawa ba.
Yace ya sanarda kakakin majalisar dokokin jihar abun da yake yunkurin yi. Amma abun mamaki kawai sai ya ji cewa sun tattauna batun a zauren majalisa. Yace bisa ga doka gwamna ya kamata ya ba wasikar yin murabus amma bai bashi ba. Gwamnan da kansa ya tabbatar da hakan a taron manema labarai. Yace bisa ga doka har yanzu bai sauka daga mukaminsa na mataimakin gwamna ba. Tun da kuma babu gwamna doka tace shi ne zai maye gurbin gwamnan.
Kotun ta amince da saka mukaddashin gwamnan Ahmadu Umaru Fintiri a cikin wadanda ake kara. An dage sauraran shari'ar har zuwa yau Talata.
Ga karin bayani.