Maihoras da kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist dake Bauchi a Tarayyan Najeriya Aliyu Zubairu, yayi kira ga kamfanin da ke shirya gasar wasannin kwallon kafa na Firimiya a Najeriya (LCM), da ta sake kai ziyara wasu filayen wasannin da ake fafata gasar NPFL na bana, domin wasu filayen basu da kyau bai kamata ace ana buga wasanni a cikinsu ba.
Kocin na Wikki ya bayyana hakane tabakin Jami'in watsa labaranta Nasiru Abdullahi Kobi, jim kadan bayan an tashi a wasan da kungiyar ta shirya da akayi da Bendel Insurance a jihar Benin, inda aka doke Wikki daci 2-0 cikin wasan mako na 13 a gasar firimiyar Najeriya 2018/2019.
Aliyu yace rashin kyawon filin wasa shi yasa aka doke kungiyartasa.
Kocin yayi kira da babbar murya na ganin hukumar ta duba koken nasa dan daukan matakan gyara a duk wani filin wasa da baya da kyau.
Zubairu ya yaba da irin salon wasan da 'yan wasansa suka buga a wasan, inda aka tafi hutun rabin lokaci babu ci, Bendel Insurance ta jefa dukka kwallayenta biyun ne bayan an dawo hutun rabin lokaci.
Daga karshe yayi gargadi ga 'yan wasannasa da su kara zage damtse, a wasanninsu na gaba musamman yadda zasu buga wasanni biyu a gida tsakanisu da kungiyoyin Lobi Stars, da Remo Fc, Wikki dai tana buga wasannin tane a filin wasa na Fantami dake jihar Gombe, sakamakon gyara da akeyi a filinta na Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi.
Facebook Forum