Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles, ta ce babu wata kasa da za ta raina a wasan zakaru na shiga gasar cin kofin duniya 2022, a cewar Patrick Pascal.
Kungiyar ta Super Eagles ta fara shirye-shiryenta ne don tunkarar gasar cin kofin Duniya da za’a yi a Qatar, wanda zai gudana a watan Oktoban 2022.
Za ta kara ne tsakaninta da Liberia, a karo na uku kungiyar na rike da kambun a nahiyar Afirka a rukunin C da rukuni na biyu a Afirka, tare da Cape-Verde, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Liberiya a wasannin da aka gudanar.
‘Yan Najeriya dai a shirye suke su kai ga zagayen karshe don daukar wannan kofin, "duk mun san cewa babu kananan kungiyoyi a Afirka.
Kowace kasa na son fidda kitse wuta, don haka kungiyar ba za ta raina kwazon kowace kuginya ba a yayin wannan gasar.
"Muna da kungiyar matasa masu kyau a yanzu, kuma 'yan wasan a shirye suke su bayar da gwargwadon karfinsu ga kasar a duk lokacin da aka kira su su yi.
Ya kara da cewa, "ina da kwarin gwiwa cewa kwararrun 'yan wasan za su tabbatar da cewa Super Eagles ta fafata a Gasar cin Kofin Duniya na 2022 a Qatar tare da goyon bayan Hukumar Kwallon kafa ta Najeriya (NFF) da kuma gwamnatin kasar."
Facebook Forum