Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Hannunmu A Kwarmata Sautin Muryoyin Obi, Oyedepo - NCC


Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP a Najeriya, Mr. Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP a Najeriya, Mr. Peter Obi

Yayin da magoya bayan Obi suke ikirarin hada sautin aka yi don a bata masa suna, wasu na cewa da ma Obi mutum ne mai nuna banbancin addini.

Hukumar da ke sa idon kan kamfanonin sadawar ta NCC a Najeriya, ta nesanta kanta daga zargin da wasu ke yi cewa tana da hannu wajen kwarmata sautin muryar da aka ji ta dan takarara shugaban kasa na jam’iyyar LP Peter Obi da Bishop David Oyedepo suna tattaunawa.

Cikin tattaunawar ta wayar tarho, an ji Obi yana neman Bishop Oyedepo da ya taimaka masa wajen samun kuri’un Kiristocin yankin kudu maso yammacin Najeriya, inda ya kwatanta lamarin da “yaki na addini.”

Tun a karshen mako da sautin muryar ya fita ake ta ce-ce-ku-ce akai a Najeriyar.

Yayin da magoya bayan Obi suke ikirarin hada sautin aka yi don a bata masa suna, wasu na cewa da ma Obi mutum ne mai nuna banbancin addini.

Sai dai yayin da wasu ke zarginta da kwarmata sautin, hukumar ta NCC ta nesanta kanta da lamarin tana mai cewa, hakan ya saba dokar aiki.

Cikin wata sanarwa da NCC ta fitar dauke da sa hann Darektan Yada labarai, Reuben Muoka, hukumar ta musanta taka wata rawa a fitar da sautin.

“Kamar yadda dokar sadarwa ta Najeriya ta 2003 da sauran dokokin kasa suka tanada, hukumar ba da ikon ta bi diddigin wata tattaunawar wayar tarho.” In ji Muoka kamar yadda Channels ya ruwaito.

Kakakin NCC ya kara da cewa, hukumar ta kai rahoton wannan zargi da ake mata ga jami’an tsaro domin su gudanar da bincike su kuma dauki mataki idan ya zama dole.

Bola Ahmed Tinubu ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu, yayin da Atiku Abubakar na PDP ya zo na biyu

Dan takarar jam'iyyar LP Obi ne ya zo na uku.

Manyan jam'iyyu siyasar da suka hada da PDP da LP sun shigara da kara a kotu suna kalubalantar sakamakon zaben.

XS
SM
MD
LG