WASHINGTON, DC —
A wani taron karfafa hanyoyin da za'a yi anfani dasu a shawo kan ta'adanci a kasar Najeriya Kanal Sambo Dasuki mai ba shugaba Jonathan shawara ta fannin tsaro ya nisanta addinin Musulunci da ta'adanci.
Ta'adanci bashi karbuwa a cikin addinin Musulunci. 'Yan ta'ada na fakewa ne da Musulunci domin samun goyon bayan mutane. Kanal Sambo Dasuki ya yi wannan furucin ne a taron karfafa hanyoyin lalama wajen magance ta'adancin da kungiyar Boko Haram ke yi a kasar da sunan Musulunci. Kanal Dasuki ya kara nisanta yaki da ta'adanci a matsayin cewa yaki da Musulunci ne. Yace hadin kan fararen hula da jami'an tsaro zai iya ragewa ko kawo karshen matsalar.
Kanal Dasuki yace duk inda ake ta'adanci babu inda aka taba samun nasara ba tare da an hada kai da fararen hula ba. Yayi misali da dan jarida idan ya shiga mutane babu wanda zai san abun da ya keyi sai dai 'yan jarida 'yanuwansa. Yace haka lamarin yake a koina a duniya. Babu inda ake yaki da wani laifi sai an hada da fararen hula. Su ne zasu ga abunda ba daidai ba su fada.
Yace lokacin da ya kama aiki ya je jihohin arewa maso gabas inda ya roki al'ummomin jihohin su gayawa 'yan kungiyar Boko Haram dake cikinsu su fito a tattauna dasu kan duk matsalolinsu dake damunsu.
Taron ya samu halartar fararen hula da dama. Wani Yusuf Maitama Tuga shi ma yana ganin karfin tuwo baya kawo masalaha. Yace yaki da kai farmaki da bindigogi kawai ba zasu kaiga nasara ba. Idan kuma ana son a samu nasara dole a hada kai da jama'a kana jama'an su fadawa hukuma wadanda suka yi nadama suna son ajiye makamansu domin a yi masu ahuwa. Wadanda basu gane ba a wayar da kansu cewa Musulunci bai yadda da irin ta'adancin da suke yi ba
Maryam Lawal Uwais ta danganta kangarewar da talauci domin 'yan ta'adan sun ga irin wahalar da iyayensu mata ke ciki. Tace yakamata a dawo a taimakawa mata. A ginasu domin yara su gane cewa iadan sun yi ta'adanci sun yiwa iyayensu ne.
A wannan taron wanda shi ne irinsa na farko da Kanal Dasuki ya shirya jama'a sun bayyana yadda jami'an tsaro suka raina fararen hula. Sun ce wasu jami'an tsaron bayan sun kwankwadi barasa sai su dira kan fararen hula suna cin zarafin mutane ba gaira ba dalili. Ta hakan su kan aika mutane lahira ko su yi masu mummunan rauni. Dalili ke na da ya sa ministan harkokin shari'a ya tunasheda jami'an tsaro su bi dokar aiki sau da kafa ta hanyar mutunta hakin dan adam domin rashin yin hakan zai kaiga gurfana gaban koyu.
Ga karin bayani.