Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana haka ne yayin ziyararsa jihar Borno a karo na farko ,inda ya kai ziyara sansanin 'yan gudun hijira da ake kira Gubio camp dake cikin garin Maiduguri da wata mattatara da ake tara 'yan Boko Haram.
Da farko an shirya Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniyan zai ziyarci garin Banki da ke Karamar Hukumar Bama a jihar Borno sai dai daga bisani aka soke ziyarar.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniyan ya kuma ziyarci fadar gwamnatin jihar Borno karkashin tsauraran matakan tsaro inda ya yi takaitacccen jawabi cikin mintuna goma.
A cikin jawabinsa a fadar gwamnatin, Babban Magatakardan ya bayyana cewa, "a nan jihar Borno, na fahimci cewa, kun riga kun dauki matakin matsalolin yaki da ta'addanci, abinda aka saba gani shine, in ka ga dan ta'adda, zaka harbe shi ne kawai amma a Borno ba haka ba ne. Gwamnatin jihar Borno ta dauki matakin daidaita wannan matsalar ta wajen daidaitawa tsakanin gwamnati da jama'a. Wadanda ba su yarda da gwamnati ba, za su bi 'yan ta'adda ne, amma a wannan gabar na tabbatar cewa, gwamnatin da gaske ta ke.
rundunar-tafkin-tchadi-ta-kaddamar-da-farmakin-bai-daya-mai-take-operation-lake-sanity
Sakatare Antonio Guterres ya kara da cewa, 'na lura cewa, mutanen da su ke tsugune a sansanin 'yan gudun hijira abinda su ke bukata, eh suna bukatar barguna da kayayyakin abinci da kuma kayayyakin biyan bukatu irin na yau da kullum, amma ba shi ba ne damuwarsu. Damuwarsu a nan ita ce ,su koma garuruwansu na asali cikin mutunci da mutuntawa. Wannan babban yanayi ne, kuma muna bukatar hakan.
Bisa ga cewarsa, "babban abinda za mu iya yi domin samun zaman lafiya shi ne a mayar da wadanda su ka shiga ta'addanci a lokacin da suka samun kansu a wani halin ni'yasu, amma yanzu suke so su bada gudummuwa wajen taimakawa 'yan'uwansu maza da mata."
A nashi jawabin, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya bayyana cewa, suna bukatar babban Magatakardan wajen neman ganin an bunkasa yankin tafkin Chadi, saboda yankin na daya daga cikin wuraren da mutanen su ke dogaro ga rayuwarsu, da kuma gina wadannan wurare domin dawo da rayuwa kamar yadda ya ke a baya.
Ya kuma bukaci kungiyoyin duniya su maida hankali a kan abinda ya shafi zaizayar kasa da ya shafi sauyin yanayi, da talauci, da jahilci da rashin daidaito tsakanin al'umma wadanda ke haduwa su haifar da ayyukan ta'addanci.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa, kimanin mutane dubu 35 suka rasa rayukansu sakamakon hare hare da ayyukan ta'addancin kungiyar Boko Haram, yayinda tashin hankalin ya yi sanadin rasa matsugunan sama da mutane miliyan biyu da dubu dari.
Najeriya ce kasa ta karshe da Babban Magatakardar ya yada zango a ziyarar kasashen nahiyar Afrika da ya fara da yada zango a kasar Senegal. A jiya Litinin, Anthonio Guterres ya ziyarci Jamhuriyar Nijar inda ya bayyana damuwa dangane da tashin hankali da tada kayar baya da masu rajin jihadi su ke yi a yankin Sahel da ya bayyana a matsayin babbar barazana a duniya baki daya.
Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Bi'u cikin sauti: