Babban dan jam’iyyar Democrat a majalisar dattijan Amurka, ya fito ya nuna adawarsa da shirin gina Cibiyar al’adu ta Musulmi tare da Masallaci a kusa da inda aka kai hare-haren ta’addanci na 11 ga watan Satumba a birnin New York.
Wani kakakin Haryy Reid ya ce shugaban masu rinjayen a majalisar dattijan Amurka ya amince da cewa Gyaran Farko na Kundin Tsarin Mulkin Amurka ya kare ‘yancin yin addini. Amma yace sanatan yana mai ra’ayin cewa ya kamata a gina wannan Masallaci a wani wurin dabam.
Reid dai yana fuskantar barazanar shan kashi a zaben rike wannan kujera ta sa a watan Nuwamba.
A ranar asabar shugaba Barack Obama yace yana goyon bayan ‘yancin da Musulmi suke da shi na gina Masallaci da kuma cibiyar al’ada a filin da ba na gwamnati ba ne a birnin New York. Amma kuma yace ba zai yi furuci kan basirar yin hakan ba.
‘Yan Republican dai sun fito da kakkausar harshe su na sukar shirin gina wannan cibiya. Sanata John Cornyn yace batar basira ce a a gina Masallaci a kusa da inda aka kashe Amurkawa fiye da dubu 2 da 600. Ya bayyana shugaba Obama a zaman wanda bai san abinda ke wa Amurkawa ciwo ba a saboda abinda sanata Cornyn ya bayyana a zaman goyon bayan da shugaban yake bayarwa ga gina wannan Masallaci.
Wannan masallaci da ake takaddama a kai, wani bangare ne kawai na Cibiyar Musulunci da za a gina a kan kudi dala miliyan 100, wadda zata kunshi dakin taro ko kallo mai kujeru 500, da wuraren wasannin motsa jiki, da dakin sinima da gidan abinci, kuma za a bude shi ga kowa da kowa.
Tun da fari, magajin garin birnin New York, Michael Bloomberg, yace zai zamo ranar bakin ciki ga Amurka idan har abokan adawa suka hana gina wannan masallaci. Magajin garin na New York da sauran masu goyon bayan gina wannan Masallaci sun ce yin hakan zai taimaka wajen rage rashin fahimta a tsakanin kasashen yammaci da Musulunci.