Kudin da hukumar EFCC ta kama a wani gida a Legas ya jawo jani-in-jaka tsakanin hukumar leken asirin kasashen waje ta Najeriya wato NIA wadda tace kudaden nata ne kuma daga babban bankin Najeriya ta karbosu, furucin da shi babban bankin ya musanta.
Kakakin babban bankin Mr. Isaac Okoroafor ya fitar da wata sanarwa wadda ya sa ma hannu yana cewa bankin bashi da hannu a makudan kudaden da aka gano a wani gida dake Legas.
Bankin ya kara da cewa baya hulda da mutane ko kuma wata hukuma ta gwamnati amma yana hulda ne da bankuna masu zaman kansu ko kuma na 'yan kasuwa. Yace saboda haka babu wani dalilin hada bankin da kudaden da EFCC ta kama da NIA tace nata ne.
Yawancin 'yan Najeriya basu san hukuma NIA ba. Wasu da aka tambayesu basu san ma'anar NIA ko kuma wace hukumace ake kira hakan ba.
Dr. Sha'aibu Shehu Aliyu malami a sashen tarihi na Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria shi yace tsohon shugaban kasar Najeriya Janar Ibrahim Babangida ne ya kirkirota.Yayi hakan ne ta raba hukumar NSO zuwa gida uku. Ya kirkiro SSS dake kula da harkokin tsaron cikin gida. Ita kuma NIA aikinta shi ne ta kula da leken asirin kasashen waje tare da tsare tsaro. Sai kuma DIA wadda ke kula da bada bayanai akan sojojin kasar. NIA din Najeriya ita ce kwatankwacin CIA din Amurka.
Kawo yanzu dai babu wanda ya fito yace kudaden mallakarsa ne baicin ita NIA da kuma gwamnatin jihar Rivers.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Facebook Forum