Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Bankin Duniya ya bada Naira miliyan 53 domin sayen gidan sauro


Wasu suna hada ragan hana sauro
Wasu suna hada ragan hana sauro

Birnin tarayya Abuja ya sami tallafin yaki da zazzabin cizon sauro da gudummuwar Naira miliyan hamsin da uku daga Babban Bankin Duniya

Birnin tarayya Abuja ya sami tallafin yaki da zazzabin cizon sauro da gudummuwar Naira miliyan hamsin da uku daga Babban Bankin Duniya.

Babban bankin Duniyan ya bada gudummuwar ne ganin yadda zazzabin cizon sauro ya zama babbar matsala a Najeriya.

Sakataren sakatariyar ayyukan kiwon lafiyar al’umma a Abuja, Ademola Onakomaiya, wanda ya sanar da haka, ya bayyana cewa, za a yi amfani da kudin a wajen sani sabon shirin samar da gidan sauro mai taken “Gidan sauro biyu a kowanne gida”.

Mr. Onakomaiya ya bayyana cewa, zazzabin ciwon sauro yafi tsanani tsakanin kananan yara da shekarunsu suka gaza biyar da kuma mata masu ciki a kasashen nahiyar Afrika dake yankin Hamada abinda yake kai ga rasa rayukansu.

Bisa ga cewarshi, zazzabin cizon sauro shine sanadin rasa rayukan kimanin kashi 20% na kananan yara a a Najeriya inda kimanin kananan yara 4,000 suke mutuwa kowacce shekara ta dalilin cututukan da ake iya magancewa.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG