Babban bankin Duniya ya yi kira ga gwamnatocin Najeriya a dukan matakai su yunkura wajen shawo kan mace macen mata da kananan yara.
Darektan babban bankin a Najeriya farfesa Caroline ce tayi kiran yayin wata ziyara da ta kaiwa gwamnan jihar Enugu Sullivan Chime.
Farfesa Sage ta bayyana cewa, babu kasar da zata iya ci gaba a yanayin da ake samun yawan mace macen mata da kananan yara wadanda bisa ga cewarta, sune ginshikin ci gaban kowacce kasa.
Ta bayyana bakin ciki ganin yadda adadin mata da suke rasa rayukansu lokacin haihuwa yake karuwa duk da ci gaba da aka samu a fannin kimiyya da fasaha da kuma ilimi.
Najeriya na daya daga cikin kasashen da ake fama da mutuwar mata da kananan yara sakamakon rashin ingantaccen tsarin lafiya, rashin hanyoyin mota, karancin dakunan jinya da kuma talauci.