Rundunar Sojojin Najeriya ta karyata zargin, kakakinta janar Sani Usman Kukasheka, yace duk wanda ya fitar da wannan labarin makaryaci ne yana mai cewa bai san dalilin da yasa mutane suke yada abinda ba gaskiya ba ne.
Ya kara da cewa Fulka tana da kyakkyawan tsaro da kewayenta don haka maganar ba gaskiya ba ce “kuma muna ci gab da aiki daidai gwargwadon halidomin kiyaye rayuka da dukiyoyin jama’a ba a garin Fulka ba duk da sauran wurare da jami’an tsaro suka a yankin arewa maso gabashin Najeriya”.
Kakakin yace farfaganda ce ta ‘yan ta’adda saboda abin yakare masu shine suke neman su tayarda hakalin jama’a.
Hedkwatar Sojojin Najeriya ta yabawa Muryar Amurka bisa yadda take bada rahotanin tsaro irin wanna a Najeriya.
Wani masanin tsaro Air Commander Baba Gamawa, yace irin wadannan labarai na karya farfaganda ce na ‘yan ta’adda domin cusa tsoro a zukatan mutane domin nuna cewa suna da sauran tasiri.
Facebook Forum