Tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Babangida, ya bayar da sanarwa dauke da sanya hannunsa, yana musanta wata takardar da wani ya rubuta da sunansa, yana mai fadin cewa wannan ra'ayin marubucin ne amma ba nasa ba.
A cikin wannan wasika da aka yi ta cacar baki a kanta, an ce tsohon shugaban ya bukaci shugaba Muhammadu Buhari da kada ya nemi tsayawa takara a shekarar 2019, a maimakon haka a kyale wani matashi ya tsaya takara.
Jiya lahadi da maraice, Janar Babangida ya maida martani kan wannan wasika, inda yace ai idan yana da irin wannan ra'ayi, ya san hanyoyin da zai iya bi na sanar da wadanda suka kamata, ba sai ya fito cikin bainar jama'a yana irin wannan ikirari ba.
Wani hadimin Janar Babangida, Zubairu Idris Abdur-Rauf, yace neman gwaninta ne ya sa wanda ya rubuta wasikar, wanda aka ce wani tsohon jami'i ne a tsohuwar gwamnatin Jihar Edo, yayi abinda yayi ba tare da yawun shi Janar Babangida ba.
Wannan al'amari dai ya mamaye kafofin labarai na Najeriya tun bullarsa jiya lahadi da safe.
Ga cikakken rahoto na Mustapha Nasiru Batsari kan wannan batu
Facebook Forum