Tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB, y ace ba zai yi magana ba akan ayyana ranar 12 ga watan Yuni da gwamnatin Muhammad Buhari ta yi a matsayin ranar Dimokradiya a Najeriya.
Mai magana da yawun tsohon shugaban Malam Zubairu Abdurauf y ace hatta wasu bayanai da aka gani a kafofin sadarwa na zamani masu alaka da batun 12 ga watan Yuni da aka ce sun fito ne daga tsohon shugaban ba Gaskiya ba ne.
Malam Zubairu yace labarin kanzon kurege ne kuma karya ce mai launi bakwai domin Janar Babangida bai ce uffan akan batun ba kuma ba zai ce komi nan gaba ba. Y ace saboda haka duk abun da aka gani a yanar gizo wasu ne kawai suka kago labarin domin su sa sunan shi cikin lamarin.
Malam Zubairu y ace bai kamata a ce Janar Babangida ya yi magana akan abun da ya riga ya wuce. “Ba zai yi magana ba akan zaben ko kuma shi wanda Allah ya riga ya karbi ransa ba.
A halinda ake ciki gwamnatin jihar Neja ta ce ta goyi bayan matakin shugaba Muhammad Buhari na ayyana 12 ga watan Yuni a matsayin ranar Dimokradiya a Najeriya. Amma gwamnatin ta ce ranar ba ranar hutu ba ce a wannan shekarar kamar yadda kwamishanan labaran jihar Malam Danjuma Sallau ya shaida. Y ace ba’a sa hutu a wannan ranar ba amma gwamnan jihar da gwamnatinsa suna goyon bayan shugaba Muhammad Buhari akan maganar.
A saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani
Facebook Forum