Baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Banki Moon yana ziyara kasashen Afrika ta yamma, wadanda suke fama da anobar Ebola, inda yayi alkawarin cewa Majalisar Dinkin Duniya zata ci gaba da taimakawa wajen yaki da bular anobar.
Jiya Juma'a Mr Ban ya kai ziyara kasar Saliyo inda ya yabawa jami'an kiwon lafiya dake aiki da Ebola a zaman jarumai, kuma ya lura da mutuwar wani sannen lokita Dr Victor Willoughby, wanda a ranar Alhamis ya zama likita na goma sha daya da cutar Ebola ta kashe a kasar Saliyo.
Mr Ban yace tilas kowa ya zage dantse wajen yaki da wannan cuta.
Kungiyar Lafiya ta baiyana a jiya Juma'a cewa kimamin mutane dubu goma sha takwas da dari shidda da uku ne suka kamu da Ebola, kuma cutar ta kashe mutane dubu shidda da dari tara da goma sha biyar.
Yau Asabar aka shirya Mr Ban zai kai ziyara kasashen Guinea da Mali.
Baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, ya kai ziyara kasashen Afrika wadanda suke fama da anobar Ebola,