A sanarwar da ya fitar a Legas ofishin jakadancin Amurka, ya ce Najeriya ba ta cikin kasashen Musulmi da Amurka ta dakatar da 'yan kasar yin balaguro zuwa kasarta.
Wannan sanarwar ta zama wajibi saboda shawarar da Abike Dabiri Erewa mai ba shugaban kasa shawara akan 'yan Najeriya dake zama kasashen waje ta bayar na cewa idan ba su da abun yi takamaimai to su dakata zuwa Amurka.
Tun farko kafin wannan sanarwar shi ma ministan harkokin wajen Najeriya Mr. Geofrey Onyema ya fito fili ya shaidawa 'yan Najeriya cewa babu wani umurnin da ya hana 'yan Najeriya dake da izinin zuwa Amurka su yi hakan.
Ya ce muddin dan Najeriya nad a takardun tafiya kasar ba a hana shi ba.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Facebook Forum