Hukumar kare yaduwar cututtuka a Najeriya ta sallami gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammed a daren jiya Alhamis, bayan ta tabbatar cewa ya warke daga cutar Covid-19 da ya kamu da har na tsawon makonni uku.
Da yake jawabi bayan gabatar da sakamakon gwaje-gwajen da akayi wa gwamnan, kwamishinan ayyukan lafiya na jihar Bauchi, Dakta Aliyu Muhammed Mai goro ya ce gwamnan ya cika dukkan ka’idojin da ake so domin sallamarsa.
A nasa jawabin gwamna Bala Muhammed ya gode wa Allah da ya warkar da shi daga cutar ta Coronavirus.
Ya ce “wannan cutar ta sani na natsu na lura da cewa shugabanci alheri ne da kuma nauyi kan kowane dan adam, kuma bazan iya biyan ‘yan Najeriya kan soyayyan da suka nuna min ba lokacin da bani da lafiya.”
Shugaban maikatan gidan gwamnatin jihar ta Bauchi, Dakta Ladan Salihu ya ce warkewar gwamnan zai basu damar gudanar da ayyukan ingantattu a jihar.
Ya zuwa yanzu dai mutum 3 ne ke ci gaba da fama da cutar Covid-19 a Bauchi.
Ga karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum