Taron gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya da na jihohin kudu maso yamma, da kungiyar Fulani ta Miyyeti Allaha, da aka gudanar a jiya Litinin, an samu kyakkyawar fahimta. Don kuwa gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Odunayo Akeredolu, ya shaida cewar bai bada umurnin korar makiyaya a jihar ba.
Abu da ya ce shine duk wasu bata gari da ke cikin gandun dajin gwamnati ba tare da bin ka'ida ba, to su gaggauta barin yankin. Da kuma bata gari, don ta haka ne kawai za'a iya samun zaman lafiya a yankin.
Gwamnan jihar Kebbi Alh. Atiku Bagudu, na daya daga cikin gwamnonin da suka halarci taron, ya ce sun cinma matsaya guda, na ganin duk Fulani da yarbawa sun hada kansu, waje daya da kuma kokarin ganin duk wasu bata gari da aka gani za a hannun ta su ga hukuma.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah ta kasa, Alh. Muhammad Kiruwa, cewa ya yi akwai bukatar gwamnonin Arewa da na Kudu su dinga haduwa lokaci zuwa lokaci, don ganin an samar da hanya daya da zata kawo zaman lafiya a tsakanin al'ummar kasar baki daya.
Haka zalika shugaban kungiyar reshen jihar Oyo Alh. Ibrahim Jijji, ya ce a shirye suke su bada duk wani goyon baya, da ake bukata don ganin an samu zaman lafiya a yanki.
Jawabin bayan taron dai ya kara tabbatar da rashin ingancin rahotannin da ke yawo ta fafen sadarwa, cewar gwamnan jihar Ondo ya umurci Fulani makiyaya da su bar gandun dajin jihar.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal a cikin sauti.