Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan dake kasar Italiya na shirin kulla yarjejiniyar kwantiragi da tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Antonio Conte.
Shugaban kulob din Inter Milan Steven Zhang ya bayyana cewa, a shirye ya ke ya biya kowanne irin kudi don daukar Conte mai shekaru 49 da haihuwa.
Kawo yanzu Conte ya horar da kungiyoyin kwallon kafa har guda 8 a tarihinsa bakwai daga ciki duk a cikin kasar Italiya ne, guda daya ne kawai a wajan kasar wato Chelsea ta Ingila.
Wasu alamu na nuni da cewar Conte bashi da bukatar komawa Italiyan, ganin irin yadda ya gindaya sharadin biyansa kudi har yuro miliyan €9, a matsayin albashinsa duk shekara, da kuma a biyan masa haraji, wanda kuma idan har Inter Milan ta amince zai dara takwaransa na Juventus Massimiliano Allegri, wanda ke matsayin Koci mafi daukar albashi a Italiyan.
Matukar Inter Milan ta amince da daukar Conte, hakan na nuna cewa za tayi asarar yuro miliyan €21, wajen sallamar mai horas da tawagarta Spalletti, wanda yarjejiniyar sa da kungiyar zai kare a shekarar 2021.
Inter Milan tana mataki na uku a teburin Serei A, na kasar Italiya a wasan mako na 31, a bana da maki 57 ranar Lahadi 14 ga watan Afirilu 2019, zata ziyarci kungiyar Frosinone, a wasan mako na 32 cikin gasar Serie A.
Facebook Forum