WASHINGTON, D.C. —
Hukumar kwallon kafa ta kasar Spaniya ta bada dama ga Luis Enrique ya dawo harkar horaswa.
Enrique, wanda ya ajiye aikinsa da nufin jinyar diyarsa wadda ta riga mu Gidan Gaskiya a kwanakin baya, ana kyautata zaton zai amince da gayyatar don kai kasar Spaniya zuwa gasar cin kofin nahiyar kasashen Turai (Euro) na shekara mai zuwa.
Ana alakanta maihoraswa Enrique da karbar aiki a Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, wacce ake ganin zata raba gari da Kocinta Unai Emery, saboda rashin tabuka abun kirki a kakar wasan bana.
To sai dai yayi watsi da batun inda ya cigaba da zama ba tare da kungiyar ba.
Facebook Forum