Christina Koch 'yar shekaru 40, injiniya ce da ke zaune a garin Livinston na jihar Montana ta kafa tarihin yin zama mafi dadewa a sararin samaniya, inda ta kwashe kwana 288.
Yanzu haka ya rage mata kusan wata biyu ta koma doron kasa.
Koch ta isa filin lura da sararin samaniyar ne a ranar 14 ga watan Maris.
Wannan tafiya da ta yi, ya sa ta shafe tarihin da Peggy Whitson ta kafa a tsakanin shekarar 2016-2017.
Ana sa ran 'yar sama jannatin Koch ta shafe kwanaki 328 ne, kusan wata 11 kenan a sararin samaniyar.
Tun farko an kuduri aniyar ta yi wata 6 ne, sai dai a watan Afrilu, hukumar sararin samaniyar kasar Amurka ta tsawaita wa’adin zuwa watan Fabairu.
A shekarar 2015 zuwa 2016 Scott Kelly na kasar Amurka ya yi kwanaki 340 a sararin samaniya, wanda a tarihin kasar shi ne da ya fi dadewa a sararin samaniyar.
Sai dai mafi tsawo a tarihin duniya shi ne wata 15 wanda wani dan kasar Rasha ya yi a shekarar 1990.
Kafin wannan, a watan Oktoba ma Koch ta taba kafa wani tarihin na kasancewa a cikin tagawagar mata zalla da suka je sararin samaniya.
Wannan dai shi ne karo na hudu da Koch ta je sararin samaniya.
Facebook Forum