Akwai yuwar za'a hukunta kungiyar kwallon kafar Kamaru bangaren Mata, kamar yadda wasu mahukuntan kwallon kafa ke kira da rashin da’ar da 'yan wasanta suka nuna a yayin gasar cin kofin duniya 201, ajin mata wanda akeyi a kasar Faransa.
Yayin wasan ranar Lahadi Kamaru bayan rashin nasararta da tayi a hannun Ingila da ci 3 da nema a zagayen kasashe 16, sau biyu ‘yan wasan ta na tilasta dakatar da wasan na dan wani lokaci kafin a ci gaba, inda a bangare guda fada ya barke tsakanin ‘yar wasan gaba ta Kamaru Augustine Ejangue da takwararta ta Ingila Toni Duggan.
Hakan ya farune sakamakon wasu kwallaye da Kamaru suka sha aka haramta, daga bisanin Ingila ta sanya na ta kwallon da VAR wato na'ura mai tallafawa Alkalin wasa ya tabbatar da cin.
Kan wannan hayaniyar hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA za ta yi zama na musamman a kansu bayan kammala gasar, kawo yanzu hukumar ta FIFA ba ta bayyana ko za ta dauki matakin ladabtarwa kan tawagar ta Kamaru ba.
Shugabar kwamitin da ke kula da kwallon mata wadda suke karkashin hukumar kwallon kafar Afrika Isha, ta ce itama tana duba yiwuwar daukar matakan ladabtarwa ga Kamarun, la’akari da cewa rashin da’ar da ta nuna basuji dadi ba, kuma ya bata sunan tawagar kwallon kafar Afrika ba kawai bangaren mata ba.
Facebook Forum