Wannan sanwarwar ta biyo bayan rahotannin da suka nuna cewa, tunda aka fara yin allurar rigakafin a shekara ta 1930, mutane 12 kadai aka samu da suka kamu da cutar bayan an yi masu allurar rigakafi bayan yiwa kimanin mutane miliyan dari shida rigakafi.
Hukumar ta bayyana cewa, sanin wannan yana da muhimmanci ga matafiya da kuma kasashen da ake fama da cutar.
An kiyasta cewa kimanin mutane dubu dari biyu ne suke kamuwa da cutar yellow fever kowacce shekara. Kimanin kashi 15% na wadanda suka kamu da cutar shawara, suna fama da zazzabi mai tsanani da ciwon mutuwar gababuwa da zubar jini, kuma yawancin mutanen suna mutuwa domin ciwon shawara bashi da magani.
Allurar rigakafi ita ce kadai hanyar da tafi amfani wajen shawo kai da maganin ciwon shawara, kashi casa'in cikin dari na mutanen da aka yiwa rigakafin shawara suna samun kariya cikin kwanaki 30 da yin rifakafi.
Ciwon shawara cura ce da sauro ke yadawa, kuma ana fama da cutar a kasashe 44 na nahiyar Afirka.