Ga masu bukatar son dan-dana rayuwa a duniyar Mars! Ga wata garabasa da wani kamfanin zirga-zirgar a duniyar na kasar Spain ya samar, mai suna Astroland, wanda ya kwaikwayi yanayin duniyar ta Mars a cikin wani kogo a arewacin kasar Spain, yanzu haka an bude shi domin baki daga ko'ina a fadin duniya.
Masana kimiyyar zanen gine-gine, sun hadu sun canza wani babban kogo mai zurfi a cikin duwatsun Cantabria, a arewacin Spain mai nisan kimanin kilomita 90 yamma da birnin Bilbao. Inda suka mayar da shi irin yanayi na duniyar Mars, wanda duk mai bukatar rayuwa a duniyar Mars, zai iya ziyarta. Sun kara da cewar yadda duniyar Mars ta ke da karancin yanayi, tare da yanayi na sanyi sosai. Tashar Ares tana ba wa matafiya dama domin su gwada wannan yanayin.
Wannan kogo yana da kariya, amma dole sai sun fita domin su zagaya, don suji ya ake ji a sararin samaniya, da jin kamar kana tafiya a iska, da kuma koyan yadda ake shuka abinci a dakunan gwaje-gwaje na musamman.
Mutane 10 ne zasu iya shiga ciki a kowane zuwa. Kudin shiga kuwa ya fara daga dalar Amurka $ 6,600 ga kowanne mutum.
Kamfanin zirga-zirgar duniyar wata na Astroland ya ce tashar Ares ta cimma sassarar aiwatar da tura rukunin farko, kuma yanzu haka ya bude wasu sabbin cibiyoyi.
Facebook Forum