Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Asibitin Koyarwa Na Jami’ar Najeriya Ya Gudanar Da Shirin Gwajin Ido Kyauta


Gwajin ido
Gwajin ido

Asibitin koyarwa na jami’ar Najeriya da ke Inugu ya gudanar da shirin gwajin ido tare da bada magani kyauta.

Daruruwan jama’a ne suka amfana da wannan shirin , inda shugabar sashen ido a asibitin Farfesa Ada Aghaji ta jaddada bukatar duba lafiyar ido a koda yaushe.

Ta ce, “Kimanin mutane biliyan daya da digo daya ne ke fama da larurar makanta ko kuma ciwon ido a fadin duniya, kuma basu da hanyar samun kulawa. Saboda haka, muna so ne mu fadakar da al’umma kan lafiyar ido, kasancewa kashi casa’in cikin dari na makafi daga kasashe masu tasowa ne kamar Najeriya. Amma ana iya jinyar kashi casa’in cikin dari na abubuwan da ke janyo makanta. Yau asibitin na gudanar da wannan shirin ne don mutane su shigo su gwada idanun su kuma su karbi magani kyauta, saboda mutane da dama basu ma san suna da matsalar ido ba.”

Gwajin ido
Gwajin ido

Asibitin koyarwa na jami’ar Najeriya dai ya gudanar da shirin ne da hadin gwiwar kamfanonin hada magunguna na Oculox Pharmacy da Micronova, wadanda suka tallafa da magungunan ciwon ido daban-daban.

A hirar shi da Muryar Amurka, Injiniya Mike Eluomuno daya daga cikin wadanda suka samu kulawa, ya ce, “Na ga likita, kuma a hakikanin gaskiya, yadda suke aiki anan ya ingantu sosai. Na yi gwaji kuma an shawarce ni in samu tabarau. Lallai yadda suka kula da larurorin mu ya birge ni sosai.”

Gwajin ido
Gwajin ido

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00
XS
SM
MD
LG